An haifi Abdullahi Abdulkadir a garin Kumo, karamar hukumar Akko, cikin Jihar Gombe. Ya fara karatun Alkur'ani a wurin Malam Isa Bakin kwari, Anguwar Turmusawa, Kumo. Daga nan sai wurin Malam Hamza na Alh. Idi Basirka, a Anguwar Sarkin Yaki, Titin Bakoshi, Kumo. Yayi karatu a makarantin Islamiyya da na Nizamiyya dabam-dabam. Musamman ma Makarantin Jama'atu Izalatil Bid'ah wa Ikamatis-Sunnah, Nat. HQ Jos. Ya yi mafi yawan karatun littafan Musulunci a wurin Malam Bappah Kawu Jauro Tukur, Kumo. Da wassu Maluman da dama. Ya karanci ilimin kira'a da tajweedi a wajen Ustaz Isa Ubaidullahi Musa Kumo....